
Jam’iyyar PDP ta fuskanci koma baya a jihar Kaduna bayan ƴan majalisarta guda uku sun sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC mai mulki. Ƴan majalisar sun bayyana cewa sun koma APC ne saboda gamsuwa da tsarin mulkin Gwamna Uba Sani.
Gwamna Uba Sani ya tarbi sabbin mambobin a jam’iyyar, inda ya ce zai ci gaba da ƙoƙarin ganin ya yi adalci ga mutanen Kaduna. Ƴan majalisar da suka sauya sheƙa sun hada da Henry Mara (mazaɓar Jaba), Emmanuel Kantiok (mazaɓar Zonkwa), da Samuel Kambai (mazaɓar Zango).
Wannan mataki na ƴan majalisar ya jawo hankalin jama’a, inda Henry Mara ya bayyana cewa PDP ta rasa tasirinta a Kudancin Kaduna saboda nasarorin da Gwamna Uba Sani ya samu wajen samar da zaman lafiya da haɗin kai a jihar.
Haka zalika, tsohon sanatan Kaduna ta Kudu, Danjuma La’ah, ya fice daga PDP zuwa APC, yana mai cewa matakin na shi ne na ƙashin kansa. Wannan sauya sheƙa ya zo ne bayan wasu ‘yan majalisa sun sanar da komawarsu APC daga PDP.
Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa APC na samun karɓuwa a Kudancin Kaduna, wanda a baya PDP ta mamaye. Ya ce yana da burin tabbatar da daidaito da ci gaba ga kowa da kowa ba tare da la’akari da bambancin siyasa ko ƙabila ba.