Jam’iyyar APC Ta Karɓi Sabbin Mambobi 3,000 a Jihar Abia

Jam’iyyar APC ta samu karbuwa a jihar Abia bayan wasu mutane sama da 3,000 sun sauya sheƙa daga jam’iyyun adawa zuwa APC. Mataimakin kakakin majalisar wakilai, Benjamin Kalu, ya karɓi sababbin mambobin a wani taron da aka gudanar a garin Akwete.

Kalu ya bayyana cewa wannan sauya sheƙar na nuni da kyakkyawar shawara daga masu sauya sheƙa, yana mai cewa akwai karin mutane da ke shirin shiga APC nan gaba. Ya jaddada cewa jam’iyyar APC tana samun karbuwa sosai a yankin Kudu maso Gabas.

A cikin jawabinsa, Kalu ya bayyana godiya ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa ƙoƙarin da yake yi na inganta rayuwar al’umma a wannan yanki. Ya yi kira ga sabbin mambobin da su jajirce wajen tallafawa jam’iyyar da kuma goyon bayan ci gaban da za a kawo.

Wannan taron ya kasance wani ɓangare na shirin ba da tallafi na Chris Nkwonta, wanda ke wakiltar yankin a majalisar wakilai. Kalu ya yi kira ga dukkanin mambobin da su kasance masu haɗin kai da juna domin samun nasarar jam’iyyar a zabe mai zuwa.