JAMB Ta Kai Kudi Fiye da Naira Biliyan 6 Ga Gwamnati a 2024

Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Jami’o’i da Manyan Makarantu (JAMB) ta sanar da cewa ta tura Naira biliyan 6,034,605,510.69 ga asusun gwamnatin tarayya a shekarar 2024. Wannan sanarwa ta fito ne daga rahoton mako-mako da hukumar ta fitar, wanda mai ba da shawara kan harkokin yada labarai, Dakta Fabian Benjamin, ya bayyana.

A cikin rahoton, JAMB ta bayyana cewa ta samu jimillar kudaden shiga na Naira biliyan 22,996,653,265.25 a wannan shekarar. Wannan nasara ta biyo bayan rage kudin fom na Jarabawar Shiga Jami’a (UTME) da aka yi, wanda ya ba da damar karin masu sayen fom.

Dakta Benjamin ya ce wannan mataki na rage farashin fom da Naira 1,500 ya haifar da karin kudaden shiga, inda ya kai jimillar kudin da aka samu daga wannan tsari zuwa Naira miliyan 9,013,068,510.69.

Har ila yau, JAMB ta yi nuni da cewa tun daga shekarar 2016, hukumar ta bayar da gudummawar fiye da Naira biliyan 50 ga baitulmalin kasa. Wannan nasara ta nuna yadda JAMB ke gudanar da harkokinta cikin inganci da gaskiya, tare da ci gaba da bayar da gudummawa ga ci gaban ilimi a Najeriya.

Hukumar ta ce ta kasance mai himma wajen bayyana gaskiyar yadda take gudanar da kudade, tare da tabbatar da cewa duk wani kudin da aka tattara ana amfani da shi a cikin al’umma.