
Garba Datti, mataimakin shugaban APC na shiyyar Arewa maso Yamma, ya shawarci Atiku Abubakar da ya hakura da takarar shugaban kasa a zaben 2027. Datti ya yi wannan kiran ne a cikin wata wasika da ya aika wa Atiku da Malam Nasir El-Rufai.
Datti ya bayyana cewa jam’iyyar adawa ta PDP ba ta da niyyar bayar da tikitin shugaban kasa ga Atiku, don haka ya kamata ya daina kokarin hadawa da wasu ‘yan siyasa. Ya kuma shawarci El-Rufai da ya dawo cikin APC don su yi aiki tare.
Mataimakin shugaban ya yi nuni da cewa Atiku ya dauki darasi daga tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo, wanda ya zauna lafiya a gefe tun bayan barin mulki a shekarar 2015. Datti ya bayyana cewa yanzu lokaci ne da Atiku ya zama dattijo, maimakon ci gaba da takara.