
An cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin sojojin Isra’ila da ƙungiyar Hamas, wanda hakan ke nufin kawo ƙarshen faɗan da ya dade yana gudana a Zirin Gaza. Wannan yarjejeniya ta biyo bayan watanni 15 na rikicin da ya jawo asarar rayuka da dama, inda hukumar lafiya ta Gaza ta bayyana cewa sojojin Isra’ila sun kashe sama da Falasɗinawa 46,000, mafi yawansu fararen hula ne.
Jami’an Hamas da Isra’ila sun tabbatar da cimma wannan yarjejeniya, wanda ya biyo bayan tattaunawa mai tsawo da ƙasashen Amurka, Qatar, da Masar suka jagoranta. Wannan yarjejeniya ta biyu ce da aka cimma bayan wacce ta ƙare a ranar 1 ga watan Disamba, 2023.
Basem Naim, wani jami’in Hamas, ya bayyana farin ciki da cimma wannan yarjejeniya, duk da cewa ya nuna cewa hakan ya kamata an yi tun a watan Mayun bara. Yarjejeniyar za ta ba da damar sakin wasu mutane da aka yi garkuwa da su a Gaza, yayin da aka yi alkawarin sako Falasdinawa da ke gidajen yari a Isra’ila.
Ana sa ran Shugaba Joe Biden zai yi jawabi kan wannan yarjejeniya daga bisani, yayin da Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ke shirin ganawa da majalisar tsaro don amincewa da yarjejeniyar.
Harin da Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba ya haifar da farmakin sojojin Isra’ila a Gaza, wanda ya jawo asarar rayuka da lalata ababen more rayuwa a yankin. Wannan yarjejeniya ta tsagaita wuta na da matuqar muhimmanci wajen dawo da zaman lafiya a Zirin Gaza da rage radadin da al’ummar yankin ke fuskanta.