INEC Ta Gano Kuskure a Kokarin Yi Wa Sanata Natasha Kiranye

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ki amincewa da korafin da aka shigar don yi wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan kiranye, saboda rashin bayar da adireshin tuntuɓa da lambobin waya a cikin wasikar da aka aike. INEC ta bayyana cewa tsarin tunbuke ɗan majalisa yana bisa ga kundin tsarin mulki da dokokin zabe.

A cikin sanarwa da hukumar ta fitar, ta bayyana cewa akwai takardu guda shida da suka ƙunshi sa hannun fiye da rabin masu zaɓe 474,554 daga rumfunan zaɓe 902 a yankunan ƙananan hukumomi biyar. Duk da haka, masu korafin ba su cika ka’idojin da aka tanada ba, wanda ya sanya hukumar ta yi watsi da korafin.

INEC ta bayyana cewa, don ci gaba da tantance korafe-korafen, akwai bukatar a cika dukkan sharuddan da aka tanada. Hakan na nufin cewa idan aka cika ka’idojin, hukumar za ta fara tantance sa hannun daga rumfunan zaɓe tare da ba da damar wakilan masu korafi su halarci wannan tsari.

Sanarwar ta jaddada cewa tunbuke ɗan majalisa hakkin masu zaɓe ne idan sun rasa amana a kansa, kuma hukumar za ta ci gaba da aiwatar da doka wajen tantance duk korafe-korafen da suka shafi zaɓe.