
Rundunar ƴan sandan Musulunci watau Hisbah a jihar Kano ta bayyana cewa ta gudanar da ayyuka masu yawa a shekarar 2024, inda ta ƙwato kudi har Naira biliyan 212.3 ga masu su na halal. Mataimakin babban kwamandan Hisbah, Mujahideen Aminudden, ne ya bayyana hakan a wata hira da manema labarai a Kano.
Mujahideen ya ce, a shekarar da ta gabata, rundunar ta karbi korafe-korafe guda 16,939, waɗanda suka shafi rikice-rikicen aure, kasuwanci, gado, da kuma basussuka. Daga cikin waɗannan, an samu nasarar warware rikice-rikice guda 7,884, wanda hakan ya taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya a tsakanin al’umma.
Hukumar ta ce, bayan karɓar kudaden, ta bai wa masu su na halal ba tare da ɗaukar ko sisi ba, a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarinta na tabbatar da adalci da inganta rayuwar al’umma. Mujahideen ya bayyana cewa ayyukan da suka yi sun haɗa da samame 885 a fadin jihar, inda aka kama mutane 354 bisa laifuka daban-daban.
Ayyukan Hisbah sun jaddada aniyarta na rage talauci da kyautata zamantakewa, ciki har da gyaran tarbiyya da tallafa wa sana’o’i. Mataimakin kwamandan ya bayyana cewa Hisbah za ta ci gaba da aiki tare da al’umma a shekarar 2025, tare da niyyar cimma muradun da suka haɗa da wayar da kan jama’a da inganta zaman lafiya a jihar.
Majalisar dokokin Kano ta yaba da ayyukan Hisbah, kuma tana shirin ƙara masu albashi da alawus-alawus, domin ƙarfafa gwiwar su wajen gudanar da aikinsu. Wannan yana nuni da yadda gwamnatin jihar ke goyon bayan kokarin Hisbah na tabbatar da adalci da zaman lafiya a jihar Kano.