
Muhammadu Sanusi II, ya yi kira ga al’ummar jihar Kano da su kwantar da hankulansu tare da guje wa tayar da tarzoma. A cikin addu’o’in da ya yi, Sanusi II ya roƙi Allah ya mayar wa masu son tayar da fitina a jihar da aniyarsu.
A cikin wani bidiyo da masarautar Kano ta fitar, Sanusi II ya yi addu’o’in samun zaman lafiya a jihar, wacce ta kasance a cikin halin rashin tabbas saboda rigimar sarauta tsakanin sarakunan biyu. Ya yi kira ga al’ummar Kano da su tankawa duk wanda ya takale su da faɗa, yana mai jaddada cewa halayyar mutanen da aka yi nasara a kansu ne.
Sarkin na Kano ya yi addu’o’in cewa, “Duk wanda yake neman ya hura wuta a Kano, Allah ya sa wutar ta ƙone shi,” tare da jaddada cewa mutane su ci gaba da yin addu’o’i, musamman a watan Ramadan.
A yanzu haka, akwai damuwa game da yiwuwar hana Sanusi II gudanar da hawan Sallah, wanda wani ƙwararren lauya, Chidi Odinkalu, ya bayyana a matsayin tabbacin da zai ba da damar gudanar da hawan Sallah ƙarama ga Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero.
Sanusi II ya yi kira ga al’umma su guje wa tashin hankali, yana mai cewa, “Insha Allahu duk wanda yake jayayya da hukuncin Allah ba zai je ko’ina ba.”