
Garin Boto da ke jihar Bauchi ya shiga cikin tashin hankali bayan rasuwar wani sabon ango da yayar amaryar sa a wani hatsarin mota da ya faru mintuna 30 kafin a daura auren su. Ango, Abba Musa, da yayar amaryar, Maryam Suleiman, sun rasu a lokacin da suke kan hanyarsu zuwa wurin bikin.
Shaidu sun bayyana cewa hatsarin ya faru ne a yayin da angon da yayar amarya ke hanyarsu daga Murno zuwa wurin da aka shirya bikin a Boto. Wannan mummunan lamari ya girgiza al’ummar garin, musamman ma ‘yan uwa da abokai da suka taru domin shaida wannan biki.
Wani ɗan uwan ango, Saminu Boto, ya bayyana cewa lamarin ya girgiza dukkan al’ummar yankin, inda ya ce, “Wannan babban rashi ne da ba za a iya mantawa da shi ba.” Ya jaddada cewa gidan amarya, wanda ya kamata ya kasance cikin shiri da farin ciki, yanzu ya koma wurin kuka da alhini.
An gudanar da jana’izar mamatan kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, yayin da al’umma ke cikin bakin ciki mara misaltuwa. A halin yanzu, amarya Raihanatu Suleiman na cikin mummunan yanayi bayan rasa angon da aka yi niyyar ɗaura auren su.
Wannan hatsari ya jawo hankalin mutane da dama, inda suka bayyana wannan rana a matsayin ta bakin ciki a tarihin yankin. Al’ummar Boto na ci gaba da bayyana alhini da kuma jimamin wannan rashi mai gir