
Sanata Kabiru Garba Marafa daga jihar Zamfara ya yi gargadi kan makomar Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa zai fuskanci ƙalubale wajen samun goyon bayan ‘yan Arewa a zaɓen 2027. Wannan magana ta fito ne a yayin da Marafa ke bayyana damuwarsa game da yadda gwamnatin Tinubu ke watsi da bukatun al’ummar Arewa.
Marafa, wanda a baya ya kasance babban mai goyon bayan Tinubu a yakin neman zaɓe na 2023, ya zargi gwamnatin da rashin bayar da muhimmanci ga yankin Arewa. Ya ce akwai barazanar Tinubu zai rasa goyon bayan yawancin ‘yan Arewa idan abubuwan da ake gani yanzu ba su canza ba.
A cikin jawabin da ya yi, Marafa ya lissafa tabarbarewar tsaro da gaza kammala manyan ayyuka a Arewa a matsayin dalilan da ke haifar da rashin jin daɗin al’umma. Ya ce, “A cikin shekaru biyu, ban ga wani babban aiki da aka kammala wa Arewa ba,” yana mai jaddada cewa gwamnatin Tinubu ta kasa tabbatar da adalci ga yankin wajen rabon ayyuka da damar cigaba.
Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ya musanta zargin Marafa, inda ya ce an raba ayyukan gwamnati a shiyyoyin kasar nan ba tare da nuna wariya ba. Duk da haka, Marafa ya dage cewa akwai bukatar gwamnatin Tinubu ta maida hankali wajen tabbatar da an gudanar da ayyukan da suka dace a Arewa.
Wannan gargadi na Marafa na nuna cewa jam’iyyar APC na fuskantar kalubale mai girma a yayin da take shirin zaɓen 2027, musamman idan ba ta yi wa al’ummar Arewa adalci ba.