
A ranar Juma’a, 17 ga Janairu, 2025, wasu ƴan damfara ta yanar gizo, wanda aka fi sani da ƴan Yahoo Boys, sun kai hari kan jami’an hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziki ta’adi (EFCC) a jihar Anambra. Wannan harin ya faru ne yayin da jami’an EFCC suka je wajen da ake zargin ƴan damfarar na gudanar da aikinsu.
Wani jami’in hukumar EFCC ya rasa ransa a wannan harin, yayin da wani daga cikin tawagar ya samu mummunan rauni kuma yana cikin mawuyacin hali a asibiti. Rundunar ‘yan sandan jihar Anambra ta tabbatar da cewa ta kama wasu daga cikin wanda ake zargi da kuma kwato makamin da aka yi amfani da shi a harin.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Tochukwu Ikenga, ya bayyana cewa suna gudanar da bincike kan wannan lamari mai tayar da hankali. Ya ce, “Muna kan bincike don gano haƙiƙanin abin da ya faru, kuma an kama wanda ake zargi.”
Harin ya yi sanadiyyar jikkatar jami’in EFCC da ya kammala wata jarabawar karin matsayi kafin faruwar lamarin. Wannan lamari na nuna yadda ƴan damfarar ke da karfi a wasu yankuna, lamarin da ke jawo bukatar daukar matakan tsaro na musamman.
Hukumar EFCC ta yi kira ga al’umma da su yi hattara da ƴan damfarar, tare da neman hadin kai don magance wannan matsalar da ke addabar al’umma. Wannan harin ya sake jaddada bukatar inganta tsaro da kuma karfafa gwiwar jami’an tsaro a fadin kasar.