Wednesday, April 30Labarai Masu Muhimmanci

Harin Ƴan Bindiga Ya Kashe Mutum 11 a Jihar Benue

A jihar Benue, ƴan bindiga sun kai hari a kauyen Anwase, inda suka kashe mutane 11, lamarin da ya jawo fushi daga gwamnan jihar, Hyacinth Alia. Gwamnan ya bayyana cewa wannan harin mummunan abu ne kuma ya yi alkawarin hukunta duk wanda aka samu da hannu a cikin wannan aika-aika.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Tersoo Kula, ya fitar, Alia ya miƙa sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu, tare da fatan samun lafiya ga wadanda suka jikkata. Gwamnan ya ce, “Za ku girbi abin da kuka shuka,” yana mai jaddada cewa ba za a bar wannan danyen aiki ya wuce ba.

Gwamna Alia ya bukaci hukumomin tsaro su kara zage dantse wajen gudanar da bincike da nufin kamo masu laifi. Ya bayyana rashin jin dadinsa game da harin da ake kai wa mutanen jihar, duk da kokarin gwamnatin sa na tabbatar da zaman lafiya.

Wannan harin ya haifar da cece-kuce a jihar, inda al’umma ke kiran a yi gaggawar daukar mataki don kare rayukan jama’a daga hare-haren ƴan bindiga. Gwamnan ya yi kira ga dukkanin masu ruwa da tsaki su hada kai wajen yaki da wannan matsala da ta addabi jihar.