Hare-haren Ƴan Bindiga Sun Tashi a Abuja, Sun Sace Hakimin Dnako da Jikokinsa

Wasu ƴan bindiga sun afka garin Dnako da ke yankin Bwari a Abuja, inda suka sace Hakimin garin, HRH Etsu Yuda Garba, tare da jikokinsa biyu, Ephraim da Philemon. Wannan harin ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin mazauna yankin da suka shaida lamarin.

Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa ƴan bindigar sun shigo garin da misalin karfe 12:03 na dare, dauke da manyan bindigogi. Sun yi harbi a cikin garin don tsoratar da mutane kafin su kutsa cikin gidan hakimin.

Wani mazaunin yankin, Tanko Baba, ya bayyana cewa ƴan bindigan sun kai hari kan gidaje hudu kafin daga bisani su sace hakimin. Ya ce, “Sun yi shiri sosai, wasu daga cikin su ma sun sanya kayan sojoji domin rudar jama’a.”

Bayan sun ɗauki hakimin, ƴan bindigar sun nufi dakunan jikokinsa, inda suka tasa keyarsu ba tare da wata-wata ba. Hakan ya janyo fargaba a tsakanin mazauna yankin, yayin da ƴan bindigar suka yi barazanar harbe-harbe kafin su tsere.

Duk da kokarin jami’an tsaro na bin sahun ƴan bindigan, ba a samu ceto wadanda aka sace ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto. Wani jami’in ‘yan sanda da ke Bwari ya tabbatar da aukuwar lamarin, amma ya ce karin bayani na hannun rundunar ‘yan sandan Abuja.

Yankin Bwari na fama da hare-haren ƴan bindiga, lamarin da ke kara tayar da hankalin mazauna. Jama’a sun bukaci gwamnatin Abuja da ta dauki matakan gaggawa domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma daga hare-haren ta’addanci.