Hare-Hare a Benue: An Kashe Mutane 26 a Makurdi da Katsina-Ala

An kashe akalla mutane 26 a hare-haren da ‘yan bindiga suka kai a kananan hukumomin Makurdi da Katsina-Ala na jihar Benue a daren ranar Alhamis.  Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun shiga gidaje tsakanin ƙarfe 12 na dare zuwa 2 na safe, ɗauke da makamai, inda suka yi wa mutane kisan gilla.

A yankin Mtswenem da Akondotyough Bawa da ke yankin North Bank a Makurdi, an kashe mutane 25.  Wani mutum kuma ya rasa ransa a wani harin daban da aka kai a Kenvanger da Agbami a gundumar Mbatyula ta ƙaramar hukumar Katsina-Ala.

Shaidu sun bayyana cewa maharan sun shiga gidaje suna harbi ba kakkautawa, inda suka kashe mata da yara.  Wasu mazauna yankin sun tsere, amma da yawa sun rasa rayukansu.  An ruwaito cewa wasu daga cikin waɗanda suka jikkata sun mutu a kan hanyarsu ta zuwa asibiti.

A Katsina-Ala, ‘yan bindigan sun yi ƙoƙarin yi wa wasu mata masu shayarwa fyaɗe, amma sai maza suka kawo ɗauki bayan sun ji kururuwarsu.  A yayin artabu da ‘yan bindigan, an kashe mutum ɗaya, wasu kuma suka jikkata.

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Benue ta tabbatar da faruwar lamarin, kuma ta ce ta tura jami’anta zuwa yankunan da abin ya shafa domin dawo da zaman lafiya.  Kakakin rundunar, DSP Udeme Edet, ya yi kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu, tare da alƙawarin cewa za a fitar da ƙarin bayani nan ba da jimawa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *