Hankalin Tinubu Ya Tashi da Jin Labarin Mutuwar Yara 35

Shugaban kasa Bola Tinubu ya nuna damuwarsa da jin labarin mutuwar yara 35 a wani taron wasanni a Oyo. Tinubu ya umarci hukumomi da gwamnatin jihar Oyo da su gudanar da bincike cikin gaggawa domin tabbatar da adalci.

Tinubu ya jaddada muhimmancin tsaron yara da duba tsare-tsaren tsaro a duk lokacin da al’umma za su gudanar da taron jama’a. A cikin wata sanarwa daga mai magana da yawun shugaban, Bayo Onanuga, an bayyana cewa Tinubu ya bayar da sakon ta’aziyya ga iyalan da suka rasa ‘ya’yansu a wannan mummunan al’amari.

Shugaban kasar ya umarci gwamnatin Oyo da ta dauki matakan da suka dace don hana faruwar irin wannan lamari a nan gaba. Matakan sun haɗa da tabbatar da bin dokokin tsaro da kuma kula da lafiyar duk masu halartar taron, musamman yara.

A halin yanzu, rundunar ‘yan sanda ta fara gudanar da bincike kan mutuwar yara 35, inda aka kama wasu mutane don gudanar da karin bincike. Wannan lamari ya jawo hankalin al’umma da kuma bukatar inganta tsaro a dukkan tarukan jama’a.