
Tsohon dan takarar shugaban kasa, Manjo Hamza Al-Mustapha, ya bayyana damuwarsa game da halin da Najeriya ke ciki, yana mai cewa shugabanni sun yi watsi da talakawa. Wannan bayani ya biyo bayan ganawarsa da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, wanda aka yi rade-radin haɗakar jam’iyyun adawa.
A cikin ganawar, Al-Mustapha ya ce har yanzu ba a fahimci irin barnar da aka yi wa rayuwar ‘yan Najeriya ba, yana mai cewa wannan ba zai yiwu ba sai a nan gaba. Ya bayyana cewa haduwarsu ta biyo bayan damuwar da ke cin zarafin al’umma, inda ya nuna cewa akwai bukatar a tattauna kan hanyoyin da za a bi don inganta halin da ake ciki.
Al-Mustapha ya koka cewa wasu shugabanni, musamman masu ilimi, ba su san irin ta’adin da aka yi wa kasa ba, har sai an jima. Ya ce, “Masu ilimin ma da yawa ba su san irin ta’adin da aka yi wa kasa ba, sai nan gaba za su fahimta.”
Ya kuma jaddada cewa wannan ganawa ba ta yi nufin jam’iyya ba, amma domin tattauna makomar kasar da yadda za a fuskanci matsalolin da suka addabi Najeriya. Al-Mustapha ya yi kira ga masu kishin kasa da su hada kai domin nemo mafita daga mawuyacin halin da ake ciki a yau.