Hafsan Sojojin Najeriya Ya Yi Alkawarin Kawo Karshen ‘Yan Lakurawa Nan Ba Da Jimawa Ba

Babban hafsan sojojin ƙasa na Najeriya, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba, ƙungiyar ‘yan ta’addan Lakurawa za a kawo ƙarshensu a ƙasar nan. Oluyede ya yi wannan bayani ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a fadar shugaban ƙasa, bayan wata ganawa da Shugaba Bola Tinubu.

Olufemi Oluyede ya kwantar da hankalin ƴan Najeriya kan barazanar ‘yan Lakurawa a yankin Arewa maso Yamma. Ya tabbatar cewa gwamnatin Najeriya da ƙasashen makwabta suna haɗa kai wajen murkushe wannan ƙungiya ta ‘yan ta’adda.

A cewar Oluyede, “A nan Najeriya muna ragargazarsu, sannan da zarar an ba su wuta a Najeriya, suna tserewa zuwa Jamhuriyar Nijar.” Ya jaddada cewa yanzu da Nijar ta huro musu wuta, hakan na nufin cewa za a shafe tarihin ‘yan Lakurawa nan ba da dadewa ba.

Hafsan ya nuna cewa haɗin gwiwa da ƙasashen dake makwabta da Najeriya yana da matuƙar muhimmanci domin tunkarar barazanar da ‘yan ta’addan ke yi. “Ya kamata mu haɗa kai da ƙasashe makwabta domin su ma lamarin ya shafe su. Ta hanyar yin aiki tare, za mu iya magance barazanar yadda ya kamata,” in ji shi.

Wannan sanarwa ta Laftanar Janar Olufemi Oluyede na nuni da cewa hukumar sojin Najeriya na da niyyar daukar matakai masu karfi wajen kawo karshen matsalar ‘yan ta’adda a ƙasar. Samun zaman lafiya da tsaro a Najeriya na daga cikin manyan burin gwamnatin yanzu.