
Gwamnonin jam’iyyar PDP sun shiya shirin shigar da ƙara a kotu domin ƙalubalantar dokar ta baci da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya ayyana a jihar Ribas. Wannan mataki na gwamnonin na nufin dawo da gwamna Siminalayi Fubara da mataimakinsa cikin mulkin jihar.
A ranar 18 ga Maris, 2025, Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta baci a Ribas, yana mai cewa hakan ya zama dole saboda rikicin siyasa da lalata kayayyakin mai a jihar. Gwamnonin PDP daga jihohin Bauchi, Adamawa, Bayelsa, Enugu, Osun, Filato da Zamfara ne za su jagoranci shigar da wannan ƙara.
A taron da gwamnonin PDP suka gudanar ta yanar gizo, sun bayyana cewa suna son kotu ta soke wannan dokar ta baci, bisa ga hujjojin da suka gina kan kundin tsarin mulki wanda ke nuna cewa Shugaban Tarayya ba shi da hurumin dakatar da gwamnati da aka zaɓa ta hanyar dimokuradiyya.
Gwamnonin na PDP na roƙon kotu da ta soke naɗin mai mulkin rikon kwarya na jihar, Ibok-Ete Ibas, suna mai cewa wannan naɗin ba bisa ka’ida ba ne. Sun yi kira ga kotun da ta tabbatar da cewa sanarwar dokar ta baci ba ta bi ƙa’idojin da doka ta tanada ba.
Ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris, ya tabbatar da cewa Shugaban Kasa na da niyyar janye dokar ta baci idan an samu daidaito a jihar.