Gwamnonin PDP Sun Ba NWC Watanni Uku Su Shirya Taron NEC

Gwamnonin jam’iyyar PDP sun ba shugabannin jam’iyyar na ƙasa watanni uku su shirya taron kwamitin zartarwa watau NEC. Shugaban kungiyar gwamnonin kuma gwamnan Bauchi, Bala Mohammed ne ya bayyana haka a wata sanarwa bayan taron da suka yi a Filato.

Gwamnonin sun nuna damuwa kan yadda ake ta jinkirin kiran taron NEC, inda suka ce hakan na kawo cikas ga ci gaban jam’iyyar. Sun kuma jaddada cewa taron na da matukar muhimmanci domin tattauna batutuwan da suka shafi jam’iyyar, ciki har da naɗin sabon shugaban jam’iyya na kasa.

A cewar Gwamna Bala Mohammed, “Ya kamata a shirya taron NEC domin ɗaukar matakan da suka dace don ci gaban jam’iyyar.”

Gwamnonin sun kuma bukaci NWC ya yi amfani da wannan lokaci wajen tuntubar masu ruwa da tsaki a jam’iyyar domin samun shawarwari kan batutuwan da za a tattauna a taron NEC.

Wannan mataki na gwamnonin PDP ya zo ne a daidai lokacin da ake ta cece-kuce kan shugabancin jam’iyyar. Tun bayan saukar tsohon shugaban jam’iyyar, Iyorchia Ayu, ana ta takaddama kan wanda zai maye gurbinsa.