
Gwamnonin jihohi 36 na Najeriya, karkashin kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF), sun bayyana jimami da alhininsu bisa rasuwar manyan dattawan ƙasa guda biyu, Cif Edwin Clark da Ayo Adebanjo. Wannan sanarwa ta fito ne daga bakin shugaban kungiyar, AbdulRahman AbdulRazaq, wanda shine gwamnan jihar Kwara.
A cikin wani taron manema labarai, AbdulRazaq ya bayyana cewa mutuwar waɗannan dattawa babban rashi ne ga ƙasar, musamman duba da irin rawar da suka taka wajen ci gaban dimokuradiyya a Najeriya. Ya miƙa sakon ta’aziyya ga al’ummar jihohin Ogun da Delta, inda mamatan suka fito, tare da addu’ar samun salama da juriya ga dukkannin danginsu.
Ayo Adebanjo, jagoran kungiyar al’adun Afenifere, ya rasu a ranar Jumma’a da ta gabata, yana da shekaru 96. Marigayin ya kasance a sahun gaba wajen fafutukar kare muradun Yarbawa da yaki da mulkin danniya a Najeriya.
Haka zalika, Edwin Clark, wanda ya jagoranci kungiyar PANDEF ta Kudu maso Kudu, ya rasu a ranar Talata, 18 ga watan Fabrairu, 2025, yana da shekaru 97. Clark ya kasance fitaccen mai rajin kare hakkin ‘yan yankin Niger Delta, musamman batun raba arzikin ƙasa.
Kungiyar gwamnonin ta bayyana cewa irin gudunmawar da waɗannan dattawa suka bayar ga Najeriya ba za a manta da ita ba, kuma tarihi zai ci gaba da tunawa da su a matsayin shugabanni na gari da suka tsaya tsayin daka wajen kare haƙƙin al’umma da tabbatar da adalci.
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, kuma ya yi alhinin mutuwar Edwin Clark, inda ya bayyana marigayin a matsayin mutum mara tsoro da ya bayar da gudummuwa mai yawa ga Najeriya a zamanin rayuwarsa.