
Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya jagoranci kaddamar da sabbin askarawa 5,000 a jihar Benue, a matsayin wani mataki na yaki da ‘yan bindiga. Taron kaddamar da askarawan ya samu halartar manyan shugabanni daga jihohin Arewa, ciki har da wakilan gwamnatin tarayya.
A cikin sanarwar da mai magana da yawun gwamnan jihar Gombe, Ismaila Uba Misilli, ya fitar, gwamna Inuwa ya bayyana cewa shirin zai taimaka wajen magance matsalolin tsaro a jihar. Ya kuma yi kira ga haɗin kai da tallafin gwamnonin Arewa wajen tabbatar da zaman lafiya.
Gwamnan ya yabi Gwamna Hyacinth Alia na jihar Benue bisa kokarinsa na kafa wannan sabuwar ma’aikatar, yana mai cewa tsaro ne ginshiƙin ci gaba a kowanne fanni. A lokacin taron, an bayar da sabbin motocin aiki guda 100 da babura 600 ga hukumomin tsaro.
Mai martaba Tor Tiv, Farfesa Ortese Iorzua James Ayatse, ya yaba wa gwamna Inuwa Yahaya bisa jagorancin da ya nuna, yana mai cewa an samar da askarawan ba tare da wata manufa ta siyasa ba.
Wannan mataki yana daga cikin kokarin gwamnonin Arewa na inganta tsaro a yankin, bayan fuskantar barazanar ‘yan bindiga da ke addabar al’umma.