Gwamnatocin Arewa Sun Kafawa Kiristoci Kafa kan Rufe Makarantu a Lokacin Ramadan

Gwamnatocin jihohin Kebbi, Bauchi da Kano sun bayyana cewa ba za su canza hukuncin rufe makarantu a lokacin azumi ba. Wannan sanarwa ta fito ne a bayan wata zazzafan martani daga ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) da ta nuna damuwa kan rufe makarantun a lokacin Ramadan.

Gwamnatin Kebbi ta bayyana cewa an yanke wannan hukunci ne bayan tattaunawa da shugabannin addinai, iyaye, da sauran masu ruwa da tsaki. Mai magana da yawun gwamnan Kebbi, Ahmed Idris, ya tabbatar da cewa ba za a sauya wannan hukunci ba, saboda an gudanar da shawarwari tare da dukkan bangarorin da abin ya shafa.

A jihar Kano, Daraktan Fadakarwa na Ma’aikatar Ilimi, Balarabe Kiru, ya ce babu dalilin sauya hukuncin, domin an gudanar da taron masu ruwa da tsaki da aka haɗa da kungiyar CAN kafin yanke hukunci.

Haka zalika, Kwamishinan Ilimi na jihar Bauchi, Lawal Zayam, ya jaddada cewa hutun Ramadan yana cikin tsarin shekarar karatu, wanda aka tsara tun daga farko. Ya ce wannan hukuncin ba zai kawo tangarda ga karatun dalibai ba.

Wannan matakin na gwamnatocin ya jawo cece-ku-ce daga kungiyar Kiristoci, inda suka bayyana cewa suna shirin daukar mataki kan wannan hukunci. Gwamnatocin sun yi kira ga dukkan bangarorin da su kasance da jituwa da juna don inganta ilimi a kasar.