
Gwamnatin Tarayya ta Najeriya ta shigar da bukatar sabon bashi na dala miliyan 300 daga Bankin Duniya, domin inganta tsarin tsaron lafiya a kasar. Wannan bayanin ya fito ne daga takardun Bankin Duniya, inda aka bayyana cewa, Cibiyar Kula da Cututtuka ta Najeriya (NCDC) za ta aiwatar da wannan shiri, yayin da Ma’aikatar Kudi ta Tarayya za ta kasance mai karban bashin.
Manufar wannan shiri ita ce don kara karfin Najeriya wajen hanawa, ganowa, da kuma Bayar da agajin gaggawar na lafiyar da ka iya tasowa.
Ana sa ran za a amince da wannan bukata a ranar 30 ga watan Yuli, 2025, bayan an kammala tantancewa da kimantawa.
Shirin Tsaron Lafiya na Najeriya (HeSP) zai mai da hankali kan fadada karfin dakin bincike na zamani, inganta cibiyoyin kiwon lafiya na farko, gina cibiyoyin aikin gaggawa da kuma samar da dakunan gwaje-gwaje na motsi. Har ila yau, shirin zai hada da gina wuraren ajiyar kayan lafiya, shigar da tsarin ruwa, tsafta, da kiwon lafiya, da kuma kafa tsarin hasken rana don karfafa tsarin lafiya.
Wannan shiri yana daga cikin kokarin da ake yi na inganta tsarin lafiyar jama’a a Najeriya, bayan darussan da aka koya daga abubuwan da suka faru a baya, ciki har da annobar COVID-19. Wannan bashi na zamani yana zuwa ne a lokacin da Najeriya ke dogaro sosai da kudaden waje. A cikin watanni 18 da suka gabata, gwamnatin Tinubu ta sami bashin dala biliyan 6.95 daga Bankin Duniya.
Bayanan daga Ofishin Kula da Bashin Najeriya sun nuna cewa Najeriya na bayar da bashin dala biliyan 17.32 ga Bankin Duniya, inda kungiyar Raya Kasa (IDA) ta bayar da dala biliyan 16.84 daga ciki. A cikin watanni tara na farko na shekarar 2024, Najeriya ta kashe dala biliyan 3.58 wajen biyan bashin waje, wanda ya karu da kashi 39.77% daga dala biliyan 2.56 a lokacin da ya gabata.