
Gwamnatin tarayya ta Najeriya ta sanar da shirin ta na sayen magunguna ga ‘yan Najeriya domin inganta kiwon lafiya da rage nauyin farashin magunguna. Wannan sanarwa ta fito ne daga Ministan Lafiya, Farfesa Muhammad Pate, a yayin bikin kiwon lafiya da aka gudanar a Abuja.
Farfesa Pate ya bayyana cewa an tanadi karin dala biliyan 3 domin tallafawa tsarin kiwon lafiya daga shekarar 2024 zuwa 2026. Wannan mataki na nufin tabbatar da cewa jama’a suna samun magunguna a farashi mai rahusa a asibitocin gwamnati, tare da rage matsalar rashin magunguna.
Ministan ya ce wannan shirin zai taimaka wajen sauƙaƙa wa marasa galihu samun kulawa da magani ba tare da wahala ba. Haka zalika, gwamnatin ta yi alkawarin inganta inshorar lafiya ga marasa galihu da kuma yawan magungunan da ake samu a asibitocin.
Farfesa Pate ya kara da cewa gwamnatin Tinubu ta kafa asusun kudi na musamman domin tallafawa marasa galihu, tare da inganta cibiyoyin kula da lafiyar mata da cututtuka masu alaka da su. Wannan shiri na sayen magunguna na da nufin rage dogaro da shigo da kayayyaki daga kasashen waje.
Duk da haka, gwamnatin ta nuna cewa za a fara samar da magungunan da kayan aikin lafiya a cikin gida Najeriya, domin rage farashin sayen magunguna da sauran kayayyaki na lafiya. Wannan shiri na fatan inganta lafiyar jama’a da tabbatar da cewa kowa yana da damar samun magani cikin sauki.