
Gwamnatin Tarayya a karkashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu ta bayyana shirin kafa cibiyoyin kera kayan gini a shiyyoyi shida na Najeriya. Wannan sabon shiri na nufin rage dogaro da kayan gini daga kasashen waje da kuma bunkasa samar da gidaje masu saukin kudi ga al’umma.
Ministan Gidaje da Raya Birane, Ahmed Musa Dangiwa, ya bayyana cewa sabuwar manufa za ta taimaka wajen samar da ayyukan yi, musamman ga matasa, tare da bunkasa tattalin arzikin ƙasar. A taron da aka gudanar tare da masu ruwa da tsaki a fannin gidaje a birnin Legas, Dangiwa ya ce cibiyoyin za su kasance a jihohin Abia, Ogun, Kwara, Kano, Gombe da Delta.
Dangiwa ya bayyana cewa kafa cibiyoyin zai rage farashin kayan gini, wanda hakan zai saukaka farashin gidaje ga ‘yan Najeriya. Ya kuma jaddada cewa za a samar da matakan rage haraji da tallafi ga masana’antu don tabbatar da nasarar shirin.
Mataimakin Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan harkokin Gidaje, Sanata Victor Umeh, ya tabbatar da goyon bayan Majalisar ga wannan shiri, yana mai cewa za su samar da dokoki da manufofi da za su taimaka wajen inganta fannin gina gidaje a Najeriya.
Babban Sakataren Ma’aikatar Gidaje, Dr. Shuaib Belgore, ya bayyana bukatar inganta dokokin da suka shafi kera kayan gini, da kuma samar da rance mai sauki ga masana’antun gini, domin rage farashin kayayyaki da inganta hanyoyin sufuri.
Ana sa ran wannan shiri zai kawo sauyi mai kyau a fannin gina gidaje a Najeriya, tare da rage matsalar rashin gidaje da ke addabar al’umma.