
Gwamnatin Tarayya ta yi gargadi ga gwamnonin jihohi kan katsalandan da kudin kananan hukumomi. Ministan Shari’a, Prince Lateef Fagbemi, ya bayyana cewa duk gwamna da ya yi katsalandan ga kudaden kananan hukumomi zai iya fuskantar tsigewa daga mukaminsa.
Fagbemi ya yi wannan gargadi ne a yayin taron shekara-shekara na Kungiyar ‘Yan Jarida Masu Ruwaito Al’amuran Shari’a (NAJUC) a Abuja. Ya bayyana cewa hukuncin da aka yanke a kotu kan kudin kananan hukumomi ya ba su ‘yancin sarrafa kudaden su ba tare da cikas ba.
Haka kuma, Fagbemi ya shawarci shugabannin kananan hukumomi 774 a Najeriya kan a guji almubazzaranci da kudadensu, yana mai jaddada cewa ana bukatar su mayar da hankali kan aikinsu na kundin tsarin mulki, musamman wajen tabbatar da ingantaccen ilimi da lafiya ga al’umma.
Wannan gargadi na gwamnatin Tinubu na da matukar muhimmanci, musamman ma a lokacin da ake fuskantar kalubale a fannin gudanar da kudi a jihar. Gwamnatin na kokarin tabbatar da cewa an bi ka’idoji da dokokin da suka shafi gudanar da harkokin kudi a matakin kananan hukumomi.