
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa za a kammala aikin gina titin Abuja zuwa Kano cikin watanni 14 masu zuwa. Wannan sanarwa ta fito daga bakin ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Alhaji Mohammed Idris, wanda ya tabbatar da cewa an kammala shirin fara aiki a titin a cikin shekara guda da wata biyu.
A yayin bikin kaddamar da gyaran sashen farko na titin daga Abuja zuwa Kaduna, ministan ya bayyana cewa aikin titin an kasa shi zuwa gida uku domin samun sauƙin kammala. Sashen farko zai tashi daga Abuja zuwa Kaduna, na biyu daga Kaduna zuwa Zaria, sannan na uku daga Zaria zuwa Kano.
Ministan ayyuka, David Umahi, ya bayyana cewa aikin zai hada da gyara titin, cike gibin gefen titin, da kuma gina magudanan ruwa. Hakanan, za a samar da fitilu na hasken rana a cikin titin da aka faɗaɗa har zuwa filin jirgin sama na Aminu Kano da kuma titin Abuja zuwa Lokoja.
Gwamnatin Tinubu ta bayyana cewa wannan mataki yana da muhimmanci don inganta zirga-zirgar ababen hawa da rage lokacin tafiya daga Abuja zuwa Kano. Alhaji Mohammed Idris ya tabbatar da cewa shugaban kasa, Bola Tinubu, ya himmatu wajen ganin an kammala aikin cikin lokaci, bayan soke aikin daga tsohon ɗan kwangilar da ya yi alkawarin kammala aikin cikin shekara uku.
Da wannan sabuwar hanyar, ana sa ran cewa za a inganta harkokin sufuri a tsakanin jihohin Arewa, tare da samar da damar kasuwanci da bunkasa tattalin arzikin yankin.