
Gwamnatin tarayya ta raba Naira biliyan 102 ga jihohi 28 a ƙarƙashin shirin SABER, wanda Bankin Duniya ke tallafawa. Wannan shiri na nufin inganta kasuwanci da sauƙaƙa saka jari a Najeriya.
Sakatariyar ma’aikatar kuɗi ta tarayya, Lydia Jafiya, ta bayyana a taron wayar da kai na ƙasa game da shirin, cewa jihohi 33 sun rattaba hannu kan yarjejeniyar karbar kuɗin, inda 28 daga cikin su suka karɓi daga dala miliyan 1 zuwa 4.
Shirin SABER na da nufin inganta dokokin kasuwanci, rage wahalhalu ga masu saka jari, da karfafa ci gaban tattalin arziki a matakin jiha. Lydia Jafiya ta bayyana cewa duk da kalubalen da aka fuskanta a farkon shirin, gwamnatocin jihohi sun nuna jajircewa wajen aiwatar da sauye-sauyen kasuwanci.
Ta jaddada cewa kuɗaɗen da aka raba suna cikin wani tsari na “Prior Results Disbursements,” wanda ke nufin cewa ana bai wa jihohin da suka cika wasu sharudda tallafi.
Wannan mataki na gwamnatin tarayya na nuni da kokarin inganta tattalin arzikin Najeriya da kuma taimakawa jihohi wajen samun karin kudaden shiga da zasu inganta rayuwar al’umma. Ana sa ran wannan shiri zai kawo canji mai kyau a fannin kasuwanci da zuba jari a cikin jihohin Najeriya.