
Gwamnatin tarayya ta karyata rahotannin da ke yawo cewa ta hana jihar Rivers kuɗaɗe daga asusunta duk wata. A cewar daraktan yaɗa labarai na ofishin akanta janar na tarayya, Mista Bawa Mokwa, har yanzu ana ci gaba da bayar da kuɗaɗen na watan Oktoba waɗanda asusun gwamnatin tarayya ke rabawa jihohi da ƙananan hukumomi.
Mokwa ya bayyana cewa jihar Rivers za ta samu na ta kuɗaɗen saboda ɗaukaka ƙarar da aka yi kan hukuncin kotun da ya hana a ba ta kuɗaɗe duk wata. “Jihar Rivers za ta samu kuɗaɗen saboda ɗaukaka ƙarar da aka yi domin neman a dakatar da aiwatar da hukuncin.”
A halin da ake ciki kuma, kotun ɗaukaka ƙara dake zamanta a Abuja a ranar Juma’a ta tanadi hukunci a wasu ƙararraki biyar da suka biyo bayan hukuncin da wata babbar kotun tarayya ta yanke kan rikicin siyasar jihar Rivers. Ɗaya daga cikin ƙararrakin dai ita ce ta adawa da hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke wanda ya dakatar da babban bankin Najeriya (CBN) sakin kason jihar Rivers daga asusun gwamnatin tarayya.
Ministan harkokin kudi na kasa, Mr. Wale Edun, ya bayyana cewa dukkanin kudaden shiga ana sarrafa su ne bisa doka da tsarin da aka shimfida. Ya kara da cewa rabon kudaden shiga tsakanin gwamnatin tarayya, jihohi, da kananan hukumomi na gudana kamar yadda ya kamata, kuma babu wani sauyi ko shirin hana jihar Rivers kudaden da suka dace da ita.
A cewar ministan, wani lokaci jinkiri na iya faruwa wajen rabon kudaden shiga saboda tsarin tattalin arziki ko wasu matsaloli na tsare-tsare, amma hakan ba yana nufin an dakatar da wata jiha daga samun hakkinta ba. Ya ce gwamnatin tarayya tana kokarin tabbatar da cewa adalci da gaskiya sun mamaye rabon dukiyar kasa.
Gwamna Siminalayi Fubara ya ce rigimar siyasar da ta bullo alheri ne ga jihar domin ta samar da yancin siyasa da bunƙasar tattalin arziki.