
Gwamnatin jihar Rivers ta bayyana mamakinta kan matakin da Shugaba Bola Tinubu ya dauka na dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara. A cikin wata sanarwa, gwamnatin ta ce abin mamaki ne ganin Tinubu ya yanke hukunci na dakatar da Fubara, duk da cewa ya bar tsohon gwamna Nyesom Wike wanda ake zargi da haddasa rikice-rikice a jihar.
Kwamishinan yada labaran jihar, Warisenibo Joe Johnson, ya bayyana cewa Fubara yana gudanar da mulki bisa doka da adalci, yana mai tabbatar da zaman lafiya da ci gaban jihar. Ya kuma jaddada cewa Fubara ya kasance mai bin doka tun bayan hawansa mulki, inda ya fifita bukatun al’umma fiye da na kansa.
Gwamnatin Rivers ta yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da zaman lafiya da bin doka yayin da ake kokarin warware matsalolin da suka taso. Johnson ya ce, al’ummar jihar na bukatar goyon baya don tabbatar da zaman lafiya, kuma ba a bukatar a dakatar da gwamna mai kokarin inganta rayuwar al’umma.
Wannan lamari ya jawo hankalin jama’a da dama, wanda ya sa mutane ke ta tattaunawa kan tasirin wannan dakatarwa ga harkokin siyasa a jihar Rivers.