
Gwamnatin jihar Oyo ta bayyana shirin ta na kafa tsarin danna tarkon ƴan bindiga da ke shigowa jihar daga arewacin Najeriya. Gwamna Seyi Makinde ya sha alwashin daukar matakai masu karfi don tabbatar da tsaron rayukan al’ummar jihar.
Mai taimaka wa Gwamna Makinde kan harkokin tsaro, Fatai Owoseni, ya bayyana cewa gwamnatin jihar za ta yi amfani da doka wajen hukunta duk wani ɗan bindiga da aka kama. Wannan mataki na zuwa ne a lokacin da aka fara yada labarin cewa wasu ƴan bindiga sun fara shigowa Oyo.
Owoseni ya yi kira ga al’umma da su ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum ba tare da jin tsoro ba, yana mai tabbatar da cewa gwamnatin Oyo za ta yi duk mai yiwuwa don kare rayukan al’umma da dukiyoyinsu. Ya kuma bayyana cewa suna aiki tare da hukumomin tsaro don tabbatar da cewa ƴan bindiga ba za su sami wurin ɓuya ba a jihar.
Gwamna Makinde ya jagoranci taron majalisar tsaro domin tattauna wannan barazana tare da neman hanyoyin magance ta. Hakan ya jaddada matukar damuwa da gwamnatin jihar ke yi game da tsaron rayuka a yankin.
Gwamnatin Oyo na kuma shirin yin hadin gwiwa da makwabtan jihohi domin kare iyakokin jihar daga masu aikata laifi, tare da inganta hadin kai tsakanin shugabannin ƙananan hukumomi da sarakunan gargajiya.
Kwanan nan, gwamnatin jihar ta bayyana cewa za ta yi amfani da ikon da ta samu wajen rage cunkoson gidajen gyaran hali, tare da bayar da kulawa ga lafiyar fursunoni. Wannan na cikin shirin da gwamnatin jihar ta kaddamar don tabbatar da tsaro da inganta walwalar al’umma.