
Gwamnatin jihar Kano ta sake jaddada cewa gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ce ta jawo matsalar karancin ruwa da ake fama da ita a jihar. Gwamnatin ta ce ta gaji tarin matsaloli daga gwamnatin da ta gabata, musamman ɓarnar da aka yi wa tashoshin samar da ruwa.
Kwamishinan ruwa na jihar, Hon. Haruna Doguwa, ya bayyana cewa gwamnatin Ganduje ta yi watsi da tashoshin ruwa, har ma aka lalata wasu aka sace kayayyaki. Ya ce gwamnati za ta kashe makudan kuɗi wajen gyara waɗannan wurare domin su dawo kan aiki.
Doguwa ya nuna takaici kan yadda aka lalata tashar samar da ruwa ta farko da aka gina a Kano a 1930, da kuma tashar Challawa da Kwankwaso ya gina. Ya ce an tone bututun ruwa, an lalata ɗakunan kula da na’urori, kuma an sace famfunan ruwa.
Gwamnatin Kano ta ce wannan ɓarnar da aka yi wa tashoshin ruwa ne ya haddasa karancin ruwa a jihar. Kwamishinan ya yi kira ga al’umma da su yi haƙuri, yana mai tabbatar da cewa gwamnati na iya bakin kokarinta wajen ganin an shawo kan matsalar.