Gwamnatin Kano Ta Ware Naira Biliyan 33.45 Don Ayyukan Ci Gaba

Gwamnatin jihar Kano ta amince da ware Naira biliyan 33.45 domin gudanar da muhimman ayyuka da zasu inganta rayuwar al’umma a fannonin ilimi, kiwon lafiya, da more rayuwa. Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana hakan a taron majalisar zartarwa da aka gudanar ranar Laraba.

Ayyukan da za a aiwatar da wannan kuɗi sun haɗa da gina tituna, asibitoci, makarantu, da gidaje, duk da nufin inganta walwalar al’ummar jihar. Kwamishinan labarai, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bayyana cewa wannan mataki na nufin inganta harkokin ci gaba a jihar.

Gwamnatin ta ware N426.4 miliyan don biyan hakkokin masu share titi 2,369 na tsawon wata tara, tare da N109 miliyan da za a yi amfani da su wajen sayen JAMB ga daliban jihar. Hakanan an ware N284.1 miliyan don gina sabon asibiti na zamani a yankin Rimin Zakara.

Bugu da ƙari, gwamnatin ta kuma ware N893.1 miliyan don gyaran kwalejin Magwan da N434.3 miliyan don gyaran makarantar sakandare ta ‘yan mata (GGSS) da ke Shekara. Wannan shiri na gwamnatin Kano na nufin tabbatar da cewa al’umma suna samun ingantaccen ilimi da kiwon lafiya.

Gwamna Abba ya bayyana cewa wadannan ayyukan suna da matuƙar muhimmanci wajen inganta rayuwar al’umma da tabbatar da ci gaban jihar Kano. An bayyana cewa wannan mataki yana daga cikin shirin gwamnatin na karfafa gwiwar al’umma da bayar da tallafi ga masu fama da talauci.