Gwamnatin Kano Ta Dawo Da Rusau Kan Gine-Gine Ba Bisa Ka’ida Ba

Gwamnatin jihar Kano ta cigaba da rushe wasu gine-gine da aka gina a wuraren da aka ware na gwamnati ba bisa ka’ida ba. Wannan mataki na gwamnatin ya biyo bayan gano wurare da dama a cikin ‘Kwankwasiyya City’ da aka gina ba tare da samun amincewar gwamnati ba.

Shugaban hukumar da ke gudanar da aikin rushe-rushen, Hameed Sidi, ya tabbatar da cewa an gano fiye da gine-gine guda 10 da aka gina ba bisa ka’ida ba a wannan yanki. Sidi ya ce hukumomin sun mayar da hankali kan gine-ginen da aka yi ba tare da izini ba domin kwato filayen gwamnati da aka yi amfani da su ba bisa ka’ida.

A cewarsa, “Mun himmatu wurin tabbatar da kawo sauyi da kuma yin abin da ya dace domin yin amfani da wuraren gwamnatin kan dalilin da aka samar da su.” Hakanan, ya shawarci al’umma da su garzaya ma’aikatar filaye don sabunta takardun filayensu da suka tsufa.

Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta bayyana cewa an ba masu kadarorin wa’adi kafin fara wannan rushe-rushe, tare da jaddada cewa hukumar za ta ci gaba da kulawa da wuraren da suka yi kaurin suna wajen gina abubuwa ba bisa ka’ida ba.

Wannan mataki na gwamnatin ya jawo cece-kuce a tsakanin al’umma, inda wasu ‘yan kasuwa a Kano, musamman a kan titin Jami’ar Bayero, suka yi korafi kan yiwuwar ruguza musu wuraren sana’a.

Hameed Sidi ya tabbatar da cewa hukumar za ta ci gaba da gudanar da bincike da hukunci kan dukkan gine-gine da aka gina ba bisa ka’ida ba, don tabbatar da cewa an kiyaye doka da oda a jihar Kano.

Gwamnatin Kano ta yi kira ga al’umma su kasance masu lura da gine-ginen da suke yi a filayensu, domin guje wa irin wannan rushe-rushe a nan gaba.