Gwamnatin Jihar Ribas Ta Karyata Gayyatar Majalisar Dokoki Kan Kasafin Kudi

Gwamnatin jihar Ribas, karkashin jagorancin Gwamna Siminalayi Fubara, ta bayyana cewa ba za ta mutunta gayyatar da Majalisar Dokoki ta masa don sake gabatar da kasafin kudin 2025 ba. Wannan sanarwa ta fito daga bakin Sakataren gwamnatin jihar, Dr. Tammy Danagogo, a wata sanarwa da aka fitar a ranar 5 ga watan Maris, 2025.

Dr. Danagogo ya bayyana cewa har zuwa ranar Talata, babu wata takarda daga Majalisar Dokoki wadda ke tabbatar da bukatar sake gabatar da kasafin. Ya ce gwamnatin jihar ta samu wannan labari ne daga kafafen sada zumunta, ba daga hukumcin majalisar ba.

Majalisar Dokokin jihar, ta ba Gwamna Fubara wa’adin sa’o’i 48 don sake gabatar da kasafin kudin, bayan hukuncin kotun kolin Najeriya da ya tabbatar da sahihancin mambobin majalisar. Duk da haka, gwamnatin Ribas ta yi fatali da wannan gayyata, tana mai cewa ba ta karɓi wata takarda a hukumance daga majalisar.

A cikin sanarwar, Dr. Danagogo ya ce, “Har zuwa ƙarshen lokacin aiki a ranar 4 ga Maris, 2025, ba mu samu takarda a hukumance daga Majalisar Dokoki ba.” Wannan ya sa gwamnatin ta yi bayani cewa duk da ra’ayinsa kan hukuncin Kotun Koli, Gwamna Fubara zai bi doka kuma zai aiwatar da matakan da suka dace domin moriyar al’umma.

Gwamnatin Ribas ta ce lauyoyin gwamnati suna jiran kwafin hukuncin Kotun Koli, kuma da zarar gwamnan ya samu cikakken bayani, zai dauki matakin da ya dace.

Wannan rikici a cikin gwamnatin jihar Ribas na ci gaba da jawo hankali tare da nuna yadda al’amuran siyasa ke shafar gudanar da mulki a jihar.