Gwamnatin Jigawa Ta Kori Ma’aikata Uku a Harkokin Shari’a

Hukumar shari’a ta jihar Jigawa ta kori ma’aikata uku daga cikin aikin su saboda aikata laifuffuka da suka shafi cin amanar aiki. Hakan na zuwa ne bayan taron hukumar na 178 da aka gudanar a ranar 7 ga Janairu, 2025, inda aka amince da ladabtar da ma’aikatan da aka samu da laifin karya dokokin shari’a.

A cikin sanarwa da Abbas Wangara, daraktan yada labarai na hukumar, ya fitar, an bayyana cewa an kori ma’aikatan Iyal Ibrahim da Baffa Alhaji saboda sayar da motoci biyu da aka ajiye a matsayin shaidar kara ba bisa ka’ida ba. Wannan aikin na su ya sabawa dokokin tsarin aikin shari’a na jihar Jigawa na shekarar 2006, wanda ke tanadin hukunci ga irin wannan laifi.

Haka kuma, wasu alkalai guda uku sun samu umarnin yin murabus saboda sakacin aiki da aikata kuskuren shari’a. Wannan ya hada da alkalin kotun shari’a, Adamu Farin-Dutse, wanda aka bukaci ya yi murabus saboda amfani da karfin iko ba bisa ka’ida ba. Alkalin Muhammad Usman ma an bukace shi da ya yi murabus saboda bayar da izinin mallakar kadara ba tare da yanke hukunci ba.

Wannan mataki na hukuma na nufin tabbatar da tsaftar tsarin shari’a da inganta nagartaccen aiki a hukumar shari’a ta jihar Jigawa. Gwamnati ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da ladabtar da dukkan ma’aikatan da suka aikata rashin gaskiya a cikin aikin su, domin inganta tsarin shari’a a jihar.