
Gwamnatin jihar Kano ta sanar da fara biyan sama da N16bn ga tsofaffin kansilolin jam’iyyar APC da suka rike mukamai daga shekarar 2014 zuwa 2024. Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya kaddamar da wannan tsari na biyan hakkokin da gwamnatin Abdullahi Ganduje ta hana su.
Gwamnan ya bayyana cewa biyan hakkokin tsofaffin kansiloli ba wata alfarma ba ce, illa hakkin da ya kamata a biya. A yayin kaddamar da aikin, ya zargi gwamnatin Ganduje da watsi da bukatun jagororin da suka yi aiki a lokacin da suka rike mukaman siyasa.
A sanarwar da kwamishinan labarai na jihar, Kwamred Ibrahim A Waiya, ya wallafa, an bayyana cewa an fara biyan kudin a gidan gwamnatin jihar. Gwamna Abba ya ce wannan mataki yana da nufin tabbatar da gaskiya da adalci a cikin harkokin gwamnati.
Ya ce, “Wannan lokaci ba wani bikin al’ada ba ne; yana wakiltar jajircewarmu wajen mutunta kima da rikon amana.” Hakanan, ya ce dukan ‘yan majalisar zartaswa sun amince da biyan hakkokin tsofaffin kansiloli.
Biyan hakkokin ya shafi tsofaffin kansiloli, mataimakan shugabannin kananan hukumomi, da masu ba da shawara na musamman daga kananan hukumomi 44 na jihar. Wannan mataki ya jawo farin ciki a tsakanin tsofaffin kansilolin da suka yi wa al’umma aiki da gaskiya.