
Gwamnatin Tarayya ta sanar da sabon tsari na kayyade mafi ƙarancin shekarun da dalibai za su kai kafin su shiga makarantun sakandare. A cikin wannan sabon tsarin, an sanya shekara 12 a matsayin mafi ƙanƙantar shekaru na shiga aji na JSS1 bayan kammala makarantar firamare.
Wannan sabuwar dokar da ma’aikatar ilimi ta fitar ta bayyana cewa dalibai za su fara makarantar firamare a shekara 6, sannan su kammala a shekara 12. Wannan tsari yana nufin cewa duk dalibi zai kammala shekaru shida na firamare kafin ya wuce zuwa JSS1.
Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, ya bayyana cewa wannan mataki na da muhimmanci wajen inganta tsarin ilimi a Najeriya, musamman a makarantun da ba na gwamnati ba. Hakanan, ya nuna cewa wannan tsarin zai taimaka wajen tabbatar da cewa dukkan dalibai sun sami ingantaccen ilimi daga tushe.
Sabon tsarin yana da niyyar inganta ingancin ilimi a fadin ƙasar, wanda ke da matukar muhimmanci ga ci gaban matasa. An yi fatan cewa wannan sabuwar doka za ta taimaka wajen rage yawan daliban da ke fuskantar matsaloli a lokacin karatu.
Gwamnatin ta kuma bayyana cewa za a ci gaba da duba ingancin makarantun da ba na gwamnati, domin tabbatar da cewa suna bin ka’idojin da aka gindaya. Wannan mataki na nuna yadda gwamnatin ke kokarin inganta ilimi a Najeriya da kuma tabbatar da cewa duk matasa sun sami damar samun ilimi mai kyau.
Ameen ya rabbi allah yasa hakashine mafi alheri gamu dalibai da al umma