Gwamnati Ta Karyata Tsohon Sanata Kan Korar Ma’aikata Masu Digirin Togo da Benin

Gwamnatin tarayya ta musanta rahoton korar dimbin ma’aikatan gwamnati da suka samu digiri a jamhuriyar Benin da Togo. Wannan karyatawa ta biyo bayan zargin da tsohon sanatan Kaduna, Shehu Sani, ya yi a shafinsa na sada zumunta.

A cewar wata sanarwa da hukumar ma’aikatan gwamnatin tarayya ta fitar, babu wata takarda da ta ce a dauki wannan mataki. Shugaban sashen watsa labarai na hukumar, Taiwo Hassan, ya ce babu wani rahoto ko shawara da aka aika musu kan wannan batu.

“Idan an kawo mana rahoto, za mu duba shi bisa ka’idoji da tsari kafin daukar mataki,” in ji Hassan.

Ya kara da cewa, korar ma’aikata tana da tsari, ciki har da gayyatar wadanda abin ya shafa don bayar da hujjojin takardunsu kafin yanke shawara. Hukumar ta jaddada cikakken iko da ta ke da shi kan daukar aiki da sallama, tare da tabbatar da babu wani mataki na korar ma’aikata a boye.

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Sanata Shehu Sani ya ce: “Masu digiri daga Benin da suka yi aure suna da yara, sun fi jin radadin wannan korar. Ina kira ga gwamnati da ta samar da wata hanya ta ilimi don gyara matsalar.”

Wannan zargi na tsohon sanatan ya jawo hankalin jama’a, inda wasu suka fara nuna damuwa kan yiwuwar rasa ayyukansu. Sai dai, hukumar ma’aikatan gwamnatin tarayya ta yi gaggawar karyata wannan zargi, inda ta tabbatar da cewa babu wani shiri na korar ma’aikata masu digiri daga jami’o’in Benin da Togo.