
Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, ya musanta zargin tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, cewa jam’iyyar APC na fama da matsaloli da dama. A cewar Uzodimma, jam’iyyar APC tana cikin hadin kai da ba ta fuskanci babbar baraka kamar yadda El-Rufai ya bayyana.
A yayin taron manema labarai, Uzodimma ya ce, “Jam’iyyarmu tana da tsari mai karfi wanda ke tabbatar da hadin kai wajen yanke shawara.” Ya kara da cewa, “APC jam’iyya ce mai girma da shugabanni a dukkan matakai, kuma tana samun karin kudin shiga wanda ke ba ta damar gudanar da manyan ayyuka.”
El-Rufai ya bayyana cewa APC ta zama jam’iyya ta mutum daya, yana mai cewa an watsi da ka’idojin jam’iyyar, wanda hakan ya janyo tabarbarewar gudanarwar jam’iyyar. Amma Uzodimma ya yi watsi da wannan batu, yana mai cewa jam’iyyar a halin yanzu na ci gaba da samun goyon bayan gwamnati tare da samun nasarori a zabe.
Gwamnan ya bayyana cewa, “Muna da tsarin mu na ciki don zabe da aiwatar da dimokuradiyya, wanda yasa muke cin nasara a dukkanin zabukan da aka gudanar.” Wannan martani na Uzodimma na nuna cewa akwai sabani a cikin APC wanda ke iya shafar hadin kan jam’iyyar a nan gaba.