
Gwamnan babban bankin Najeriya, Olayemi Micheal Cardoso, ya bayyana dalilin da ya sa ma’aikata 1000 suka bar aikin bankin CBN a lokaci guda. A cewar gwamnan, ma’aikatan sun yi murabus ne bisa radin kansu, ba tare da an tilastawa ko wanne daga cikinsu ba.
Wannan bayani ya zo ne a gaban majalisar wakilan tarayya, inda Cardoso ya bayyana cewa bankin ya ba da damar sallama ga wadanda suka nemi hakan. Ya ci gaba da cewa, kowane ma’aikaci da ya bar aikin ya karbi hakkinsa kafin sallamar.
Mataimakin darekta, Bala Bello, wanda ya wakilci gwamnan a taron, ya bayyana cewa an yi wannan tsarin ne domin inganta aikin bankin, tare da tabbatar da cewa babu wanda aka tursasa ya bar aiki. Wannan bayani na gwamnan ya zo ne a lokacin da majalisar wakilai ke gudanar da bincike kan korar ma’aikatan da aka yi a bankin.
Cardoso ya kara da cewa, an samu wannan yanayi ne sakamakon bukatar jama’a da kuma tsarin da bankin ke son aiwatarwa. Har ila yau, ya ce wannan ba sabo bane a CBN, domin a baya-bayan nan ma, an sami korar wasu daraktoci.
Majalisar ta yi alkawarin gudanar da bincike mai zurfi don tabbatar da cewa an yi wa kowane bangare adalci a wannan lamari.