Gwamna Ya Roki ‘Yan Kwadago Su Hakura da Shiga Yajin Aiki

Gwamnan jihar Cross Rivers, Bassey Edet Otu, ya roki ƴan ƙwadago su haƙura da shirin yajin aikin gargaɗi da suka tsara na kwanaki biyu, wanda zai fara daga ranar Lahadi, 24 ga Nuwamba zuwa Talata, 26 ga watan Nuwamban 2024. Wannan roko na gwamnan ya biyo bayan taron da aka gudanar a filin wasa na U.J. Esuene a Calabar, inda aka gudanar da tattaunawa kan matsalolin da ma’aikata ke fuskanta.

Gwamna Otu, wanda mataimakinsa, Peter Odey, ya wakilta a wajen wannan taro, ya bayyana cewa yana da niyyar inganta jin daɗin ma’aikatan jihar. Ya yi kira ga shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC da su janye yajin aikin da suke shirin yi, tare da haɗa kai da gwamnan a ƙoƙarinsa na inganta rayuwar al’umma.

Peter Odey ya jaddada cewa Gwamna Otu na da burin samar da ingantacciyar jihar Cross Rivers ga dukkan mazaunan ta. Ya bayyana cewa gwamnan ya jajirce wajen inganta halin da ma’aikata da waɗanda suka yi ritaya suke ciki, ta hanyar biyan basussukan giratuti da biyan kuɗin fansho a kan lokaci.

Har ila yau, Gwamna Otu ya yi alkawarin samar da mafi ƙarancin albashi da ya zarce N70,000 ga ma’aikata a jihar, yana mai cewa hakan na daga cikin manufofinsa na inganta rayuwar ma’aikata da kuma ƙara musu kwarin gwiwa.

Wannan roko na gwamna ya zo ne a lokacin da ƙungiyoyin ƙwadago suka nuna rashin jin daɗi da wasu abubuwan da suka shafi biyan albashi da walwalar ma’aikata. Gwamna Otu na fatan cewa wannan tattaunawa za ta kai ga warware matsalolin da ma’aikata ke fuskanta a jihar.

Al’umma na fatan ganin ingantaccen shugabanci daga gwamna Otu, domin samun ci gaba a fannin ma’aikata da jin dadin al’umma a jihar Cross Rivers.