
Gwamnan jihar Akwa Ibom, Umo Eno, ya bayyana cewa zai fitar da jerin sunayen sabbin kwamishinoni a mako mai zuwa, sannan ya karyata jerin sunayen da aka wallafa a kafafen sadarwa a matsayin karya. Gwamnan ya yi wannan jawabin ne a wani taron bankwana da tsofaffin mambobin majalisar zartarwa.
A cewarsa, jerin sunayen da aka bayyana ba su da tushe, kuma yana mai cewa zai gabatar da sahihan sunaye ga Majalisar Dokokin jihar don tantancewa. Gwamnan ya ja kunnen masu neman shiga majalisar zartarwa da kada su nemi matsayi ta hanyar wasu mutane, yana mai cewa wannan ba zai yi tasiri ba.
Wannan mataki na gwamna ya biyo bayan sallamar dukan mambobin majalisar zartarwa da ya yi a makon da ya gabata. Gwamna Eno ya jinjina wa tsofaffin kwamishinoni bisa kyakkyawan aiki da suka yi, yana mai cewa za a sake amfani da su a wasu matakan da suka dace a nan gaba.
Ya kuma bayyana cewa sabon tsarin gudanarwa zai tabbatar da cewa wadanda za a nada sabbin kwamishinoni sun kasance masu biyayya da amana, don inganta ayyukan raya jihar da kuma tabbatar da ci gaban al’umma.