
Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya bayyana gamsuwarsa kan manufofin gwamnatin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu. A cewar gwamnan, manufofin na Shugaba Tinubu suna da nufin sake fasalin Najeriya domin samun ci gaba mai ɗorewa.
Uba Sani ya yi wannan bayanin ne a yayin wani taron tattaunawa da ƙungiyar Arewa Think Tank ta shirya. Ya jaddada cewa idan ƴan Najeriya suka ƙara juriya, za a fara ganin amfanin wadannan manufofi nan ba da dadewa ba.
Gwamnan ya bayyana cewa, duk da kalubalen da manufofin ke fuskanta, akwai alamu na ci gaba a fannin tattalin arziki, wanda ke fara farfaɗowa. Ya bayyana cewa, don cimma burin sake fasalin Najeriya, dole ne a mayar da hankali kan noma, wanda shi ne ginshiƙin tattalin arzikin ƙasar.
Uba Sani ya ce, “Shugaba Bola Tinubu ya riga ya fara nuna mana hanya. Gwamnatinsa ta fifita noma da zuba jari a wannan fanni.” Ya ƙara da cewa, wannan zuba jari yana da matuƙar muhimmanci wajen magance matsalolin talauci da rashin aikin yi a cikin al’umma.
Gwamnan ya yi kira ga dukkan ƴan Najeriya da su goyi bayan shugabancin Tinubu domin ganin an cimma nasarorin da aka sa a gaba.