Gwamna Uba Sani Ya Taya El-Rufai Murnar Ranar Haihuwarsa, Jama’a Sun Yi Tsokaci

Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya taya tsohon gwamnan, Nasir El-Rufai, murnar zagayowar ranar haihuwarsa, inda ya bayyana masa fatan alheri da kariya daga Allah. Wannan sakon taya murnar ya biyo bayan rade-radin rashin jituwa tsakanin su, wanda ya haifar da ce-ce-ku-ce a kafofin sada zumunta.

Uba Sani ya wallafa wannan sakon a shafinsa na sada zumunta a ranar Lahadi, 16 ga watan Fabrairu, 2025, bayan cikar shekaru 65 da El-Rufai ya yi. Duk da haka, sakon ya jawo mabanbantan ra’ayi daga masu amfani da kafafen sada zumunta, inda wasu ke ganin cewa Uba Sani ya ci amanar El-Rufai, yayin da wasu suka bayyana cewa hakan ya dace don nuna kwarewa a fannin siyasa.

Wasu daga cikin masu ra’ayi sun bayyana cewa ya kamata Uba Sani ya ji kunya bisa ga wannan sakon, yayin da wasu ke ganin cewa wannan mataki na nuna kyakkyawar alaka tsakanin su ne, wanda zai iya kawo ci gaba a harkokin siyasa.

A cikin sakon taya murnar, Uba Sani ya ce: “Ina mika gaisuwar taya murna da fatan alheri ga dan’uwana, abokina kuma magabaci na, Mai Girma Malam Nasir El-Rufai, a bikin zagayowar ranar haihuwarsa. Ina rokon Allah madaukaki ya ci gaba da shiryar da shi, ya kare shi, ya kuma kara masa ƙarfi.”

Wannan lamari ya jawo hankalin jama’a, inda ake ci gaba da tattaunawa kan dangantakar siyasa da ke tsakanin Uba Sani da Nasir El-Rufai, musamman a wannan lokaci na zafafan zabe da ke tafe.