Gwamna Radda Ya Kwatanta Sharuddan Karban Tuban ‘Yan Ta’adda a Katsina

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta nemi sulhu da ‘yan ta’adda a daji ba, sai dai idan sun mika wuya da kansu. Wannan jawabi ya fito ne a lokacin wani taron tallafawa al’umma da aka gudanar a karamar hukumar Jibiya.

Radda ya bayyana cewa idan ‘yan ta’adda sun ajiye makamai kuma sun yanke shawarar daina aikata laifuka, gwamnati za ta karɓe su a matsayin ‘yan kasa nagari. Ya jaddada cewa ba zai yiwu a yi sulhu da ‘yan bindiga kamar Bello Turji ba idan ba su yi tuban gaskiya ba.

Gwamnan ya kaddamar da shirin tallafin Naira miliyan 50 ga matasa, mata tsofaffi, da mabukata a yankin, wanda aka shirya don rage wahalhalun da suke fuskanta, musamman a lokacin azumin Ramadan. Ya bayyana cewa gwamnatin sa za ta tabbatar da ciyar da kimanin mutum miliyan 2.2 kafin karshen watan Ramadan, domin rage radadin da jama’a ke fuskanta.

Dikko Radda ya yi kira ga hadin kai tsakanin shugabanni da al’umma wajen shawo kan matsalolin tsaro da talauci a jihar. Hakan na nuni da bukatar gina zaman lafiya da inganta rayuwar al’umma a Katsina.