Wednesday, April 30Labarai Masu Muhimmanci

Gwamna Radda Ya Bayyana Farin Cikinsa Kan Nasarorin Sojoji a Katsina

Gwamna Dikko Umaru Radda na jihar Katsina ya bayyana gamsuwarsa kan nasarorin da dakarun soji suka samu wajen yaki da ƴan bindiga a jihar. Gwamnan ya yaba wa jami’an tsaro bisa ga ragargazar ƴan bindiga 80 a yankin Jibia.

A cikin sanarwa da kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Nasir Mu’azu, ya fitar, Gwamna Radda ya bayyana cewa sojojin, tare da haɗin gwiwar sauran jami’an tsaro, sun gudanar da hare-hare a sansanonin ƴan bindiga da ke yankunan Kadoji, Matso-Matso, Bagga, Dogon Marke da Takatsaba. Wannan aikin ya biyo bayan bayanan sirri da suka tabbatar da cewa ƴan bindiga na da sansanoni a wannan yanki.

Gwamnan ya ce, “Gwamnatin jihar Katsina tana mika godiya mai zurfi ga jajircewar tawagar tsaro ta hadaka wajen dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.” Ya kuma yi kira ga al’umma da su ci gaba da bayar da bayanai kan ayyukan ƴan bindiga don inganta tsaron yankin.

Hare-haren da aka kai a ranar Asabar, 4 ga Janairu 2025, sun haifar da rauni ga wasu ƴan bindigar, tare da lalata maɓoyarsu da muhimman kayan aikinsu. Wannan nasara ta dakarun soji na daga cikin alƙawarin Gwamna Radda na tabbatar da tsaro a jihar Katsina tun bayan hawansa mulki.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da ba da goyon bayan jami’an tsaro ta hanyoyi daban-daban don tabbatar da ɗorewar zaman lafiya a jihar da kuma yankin Arewa maso Yamma.