
Gwamnan Kebbi, Dr. Nasir Idris, ya bayyana cewa babu sansanin ƴan bindiga ko ɗaya a jihar Kebbi. Wannan bayani ya fito ne a yayin taron tsaro da ya gudanar tare da shugabannin tsaro a jihar.
Gwamnan ya bayyana cewa galibin ƴan bindigar da ke aikata ta’addanci a jihar suna shigowa ne daga jihohin makwafta, yana mai cewa Kebbi ta haɗa da jihohi uku da kuma kasashe biyu, wanda hakan ya sa miyagu ke shigowa su aikata mugun nufi.
Ya ce, “Babu wurin da ƴan bindiga suka kafa sansani a jihar Kebbi.” Gwamna Idris ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da karfafa ayyukan ƴan banga da kuma samar da ƙarin kayan aiki domin inganta ayyukansu a wannan sabuwar shekara.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa gwamnati za ta sayo babura 1,000 ga kungiyoyin ’yan banga domin inganta ayyukansu. Wannan mataki na nufin kawo karshen ayyukan ƴan bindiga da sauran miyagu a Kebbi, inda ya bayyana cewa ƴan banga suna matuƙar kokari wajen taimaka wa jami’an tsaro a yaƙi da ta’addanci.
Gwamna Idris ya bayyana cewa gwamnatin jihar Kebbi ta yi kokari matuka wajen magance matsalolin tsaro a cikin shekarar da ta gabata, tare da tsare-tsaren da za su inganta tsaro a jihar a shekarar 2025.