Gwamna Makinde Ya Sake Naɗa Prince Adebayo Adegbola a Matsayin Eleruwa

Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya amince da sake naɗa Prince Adebayo Adegbola a matsayin sabon Eleruwa na Eruwa, bayan shekaru da tsige shi daga sarauta. Wannan naɗin na zuwa ne bayan shari’ar da aka kammala kwanan nan, wacce ta tabbatar da cewa har yanzu ba a ɓaɗa sarki ba tun bayan tsige Adegbola a shekarar 2019.

Adegbola, wanda aka naɗa a matsayin sarkin Eruwa tun a shekarar 1998, ya fuskanci kalubale da dama a cikin shekaru, ciki har da shari’ar da ta soke naɗinsa a ranar 29 ga Nuwamba, 2019. Kotun Koli ta bayyana cewa an tafka rashin adalci da karya doka a hanyoyin da aka bi wajen naɗin basaraken.

A cikin sanarwar da kwamishinan yada labarai na jihar Oyo, Dotun Oyelade, ya fitar, ya bayyana cewa hukuncin da babbar kotun jihar Oyo ta yanke a ranar 22 ga Oktoba, 2024, shi ne maƙasudin da gwamnati ta yanke shawarar mayar da Adegbola kan sarautar.

Kwamishinan harkokin ƙananan hukumomi da masarautu, Hon. Ademola Ojo, ya bayyana cewa bisa doka, iyalan Laribikusi ne ke da damar naɗa sabon sarki. Duk da haka, bayan da suka kasa gabatar da sunayen masu takara a cikin wa’adin da doka ta tanada, an ba wa iyalan Akalako damar gabatar da ’yan takara.

Sabon Eleruwa, Adebayo Adegbola, ya yi alkawarin aiki tukuru domin kawo zaman lafiya da ci gaban mutanensa. Wannan naɗin ya kawo farin ciki ga al’ummar Eruwa, yayin da ake sa ran sabon sarki zai inganta harkokin masarautar da al’amuran yankin.