
Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya nada Sani Ahmadu Ribadu, dan uwa ga Malam Nuhu Ribadu, a matsayin sabon Sarkin Fufore. Wannan nadin ya biyo bayan kirkirar sababbin masarautu guda bakwai a jihar, wanda ya hada da masarautu masu daraja ta biyu da masu daraja ta uku.
Gwamna Fintiri ya bukaci sababbin sarakunan su kasance masu gaskiya, adalci, da rikon amana wajen gudanar da ayyukansu. Gwamnan ya bayyana cewa nadin sabbin sarakunan ya samu ne bisa cancanta da goyon bayan jama’a.
Sababbin sarakunan sun hada da:
- Sani Ahmadu Ribadu (Sarkin Fufore)
- Alheri Nyako (Tol na Huba)
- Bulus Luka Gadiga (Mbege na Michika)
- Ali Danburam (Ptil na Madagali)
- John Dio (Gubo Yungur)
- Aggrey Ali (Kumu na Gombi)
- Ahmadu Saibaru (Sarkin Maiha)
Wannan mataki na gwamnatin jihar ya kasance wani ɓangare na kokarin inganta tsarin masarautu domin amfanin al’umma. Gwamna Fintiri ya taya sabbin sarakunan murna, yana mai tabbatar da cewa nadin nasu ya fara aiki nan take.